Harin Ta'addanci A Kusa Da Karbala
Nov 14, 2016 11:59 UTC
Mutane 6 Ne Su ka yi Shahada A wani Harin Ta'addanci A Kusa da Karbala.
A kalla mutane shida ne su ka yi shahada yayin da wasu shida su ka jikkata a wani wuri mai nisan kilo mita 120 a kusa da Karbala.
Gwamnan Jahar Karbala, Nasif Jasim, ya bayyana cewa; Wasu 'yan ta'adda 6 sun yi kokarin kutsawa cikin karbala ta hanyar Ayunul-Tamr, mai nisan kilo mita 120 daga birkin, sai dai jami'an tsaro sun iya gane su da kuma kashe su.
Sai dai wani dan ta'addar ya shiga cikin gidan mutane, inda ya tarwatsa kansa a ciki, abinda ya yi shahadar mutane 6 da kuma jikkata wasu shida.
Tags