Saudiya na ci gaba da ta'addanci a kasar Yemen
Jiragen yakin kawancen Saudiya sun kai hari a jihar Ib ta kasar Yemen,tare da kashe mutane da dama.
Rahotani dake fitowa daga kasar Yemen sun habarta cewa a jiya Litinin Jiragen yakin kawancen masarautar Saudiya sun kai hari kan manyan motoci daukan man fetur a kauyen Yarim na Jihar Ib, harin ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 14 tare da jikkata wasu 11 na daban.
A wani kokarin na rufe ta'addancin da suka aikata, kakakin Sojin Saudiya Ahmad Usairi ya ce jiragen yakin kawancen Saudiya sun kai hari kan manyan motoci dauke da makaman 'yan hutsi a jihar Ib, saidai shaidu da ido sun karyata wannan ikrari tare da tabbatar da cewa motocin daukan man fetur ne aka kaiwa harin, kuma dukkanin mutanan da suka kashe fararen hula ne, har ila yau Jiragen kawancen Saudiyan sun yi ruwan bama-bamai a kauyen Namir da wasu yankuna kudancin kasar.
A matsayin mayar da martani, Dakarun tsaron Yemen da na sa kai sun kai hari kan sansanin Sojin Saudiya a jihar Jizan dake kudancin kasar,Tun a watan Maris din 2015 din da ta gabata ce kasar saudiya bisa goyon bayan Amurka ta fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen, bisa da'awar mayar da Gwamnatin Abdu Rabahu Mansur Hadi shugaban kasar da ya yi murabus, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar dubun dubutan fararen hula a kasar.