An sake kashe wani jami'in tsaron a kasar Saudiya
Ma'aikatar tsaron Saudiya ta sanar da sake kashe wani jami'inta a arewacin kasar
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto majiyar tsaron Saudiya na cewa jami'in tsaron ya rasa ransa ne bayan da wasu 'yan bindiga suka yi masa ruwan harsahse har 13 a yankin Tabuk dake arewacin kasar kuma tuni aka isa da gawarsa zuwa wurin ajiyar gawawwaki na asibitin garin.ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya ko wani gungu da ya dauki alhakin kai wannan hari.
A daren Assabar din da ta gabata ma wasu 'yan bindiga sun hallaka wani jami'in tsaron Saudiyan a gabashin kasar, a makunin baya-bayan nan dai jami'an tsaron Saudiya na fuskantar hare-hare daga wani gungun 'yan bindiga a yankuna daban daban na kasar.
Tun daga shekarar 2011 ne Al'ummar kasar Saudiya na yankuna daban daban suka fara nuna rashin amincewarsu kan yadda iyalan masarautar Saudiyan ke nuna rashin adalci wajen raba Dukiyar kasar.