Yeman: Zaman Farko Na Sabuwar Gwamnatin Ceton Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i14593-yeman_zaman_farko_na_sabuwar_gwamnatin_ceton_kasa
Sabuwar gwamnatin Yeman Karkashin Abdulaziz Bin Habtur ta yi zaman farko a San'aa
(last modified 2018-08-22T06:59:19+00:00 )
Nov 30, 2016 02:49 UTC
  • Yeman: Zaman Farko Na Sabuwar Gwamnatin Ceton Kasa

Sabuwar gwamnatin Yeman Karkashin Abdulaziz Bin Habtur ta yi zaman farko a San'aa

Sabuwar gwamnatin Yeman Karkashin Abdulaziz Bin Habtur ta yi zaman farko a San'aa.

Tashar Telbijin din al-masir ta kasar Yeman ta bada labarin cewa; Ministoci sun gabatar da shawarwari da kuma tsarin aiki ga pira minista a zaman da su ka yi a jiya talata da zummar gabatar da su ga majalisar dokoki.

Pira minista Abduaziz Bin Habtur, ya bukaci ministocin da su gabatar masa da shawarwarin nasu a rubuce, domin shi kuma ya gabatar da su ga majalisar dokokin kasar ga majalisar dokoki domin amincewa.

Gwamnatin Bin Habtur ta sami amincewar majalisar dokokin kasar ta Yeman, domin fitar da kasar daga matsalolin da take fama da su na tattalin arziki da tsaro.

Gwamnatin dai tana da cikakken goyon bayan kungiyar Ansarullah, da kuma Ali Abdallah Saleh.