Masar Ta Kirayi Majalisar Dinkin Duniya Ta Warware Rikicin Kasar Syria
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i14911-masar_ta_kirayi_majalisar_dinkin_duniya_ta_warware_rikicin_kasar_syria
Maa'aikatar harkkokin Wajen Masar ta bukaci a tsagaita wutar yaki a kasar Syria
(last modified 2018-08-22T11:29:21+00:00 )
Dec 06, 2016 12:06 UTC
  • Masar Ta Kirayi Majalisar Dinkin Duniya Ta Warware Rikicin Kasar Syria

Maa'aikatar harkkokin Wajen Masar ta bukaci a tsagaita wutar yaki a kasar Syria

Gwamnatin Kasar Masar ta bukaci kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, da su kawo karshen rikicin kasar S yria.

 Ma'aikatar harkokin Wajen kasar Masar, ta fitar da wani bayani a yau talata da a ciki ta bayyana cewa; Wajibi ne a ci gaba da yin kowane irin kokari domin ganin an kawo karshen rikikin da ake yi a kasar ta Syria..

Bayanin na kasar Masar, ya biyo bayan kasa cimma wata matsaya ne akwamitin tsaron a jiya litinin akan tsagaita wutar yaki a birnin Halab,          ( Aleppo).

Kasashen Birtaniya da Faransa ne dai su ka gabatar da bukatar tsagaita wutar yakin, sai dai kasashen Rasha da Chana sun hau kujerar naki.

Rashan ta ce, kasashen Birtaniya da Farasna suna son bada kariya ne ga kungiyoyin 'yan ta'addar da ke cikin birnin.