Tawagar Kungiyar Lauyoyin Kasashen Larabawa Ta Ziyarci Shugaba Assad
Tawagar kungiyar lauyoyin kasashen larabawa ta ziyarci shugaba Bashar Assad a yau a fadarsa da ke birnin Damascus, inda suka jaddada goyon bayansu ga gwamnati da kuma al'ummar Syria, wajen fuskantar 'yan ta'addan takfiriyya.
A yayin ganawar, shugaba Bashar Assad ya bayyana cewa; makiya al'ummar Syria sun bata lokacinsu da makudan biliyoyin daloli da nufin rusa Syria da al'ummarta saboda adawarsu da siyasar mulkin mallaka, amma hakan bai yi nasara ba, duk da cewa an kwaso 'yan ta'adda daga kowane sako na duniya zuwa kasar Syria domin aiwatar da wannan manufa, amma abin da ke faruwa a Aleppo a halin yanzu babbar manuniya ce kan cewa makiya ba su yi nasara kan Syria ba.
A nasu bangaren wakilan kungiyar lauyoyin kasashen larabawa wadda ta hada lauyoyi daga dukkanin kasashen larabawa, sun nuna cikakken goyon bayansu ga namijin kokarin da sojojin Syria ke yi na fuskantar 'yan ta'adda na duniya a cikin kasarsu, tare da bayyana hakan a matsayin wani aiki ne suke gudanarwa a madadin dukkanin al'ummomin larabawa da sauran al'ummomin duniya, domin kuwa a halin yanzu a duniya babu wanda ya kubuta daga barazanar 'yan ta'adda masu dauke da akidar kafirta musulmi.