Birnin Aleppo Ya Fice Daga Karkashin Ikon 'Yan ta'adda
Dec 13, 2016 06:31 UTC
Sojojin Syria Sun Kwace Birnin Halab Daga 'Yan ta'adda.
Sojojin Syria sun kawo karshen ikon 'yan ta'adda da birnin Aleppo na tsawon shekaru biyar.
Majiyar watsa labaru ta Spotnic ta sanar da cewa; sojojin na Syria sun kori kungiyoyin 'yan ta'addar ta hanyar kwace sansanin karshe da ke hannun 'yan ta'addar a cikin birnin.
Rahotanni da su ke fitowa daga cikin birnin suna nuni da cewa' mazaunansa sun bazama kan tituna cikin murna da farin ciki.
Tun kwanaki biyu da su ka gabata ne dai, sojojin na syria suka sanar da cewa suna gab da kwace birnin daga hannun 'yan ta'addar da kasashen Amurka da wasu larabawa su ke taimakawa.
.
Tags