Gargadin Majalisar Dinkin Duniya Akan Halin Mutane Yeman:
Mutanen Yeman Za su iya fadawa cikin Karin Wahala
Majiyar hukumar bada agaji ta majalisar dinin duniya ta yi gargadin cewa al'ummar kasar Yeman za su iya fadawa cikin karin wahalhalu saboda yaki da kuma tabarbarewar tattalin arzikinsu.
Babban jami'i mai kula da ayyukan bada agaji na majalisar dinkin duniya a kasar Yeman, Jimmy Mack Goldric ya ce; daidai lokacin da yakin kasar Yeman ya karaci cika shekaru biyu da farawa, fiye da rabin al'umar kasar mai mutane miliyan 28, suna fama da karancin abinci, yayin da wasu miliyan bakwai su ke fama da yunkwa.
Majiyar majalisar dinkin duniyar ta kuma ce; karancin abincin da ake da shi a cikin kasar ta Yeman ya kai ga a kira shi yunwa, domin a tsakanin kowadanne yara 10 na kasar, 8 daga cikinsu suna fama da rashin abinci mai gina jiki.
Bugu da kari Goldrick ya ce; Mutane miliyan 18.8 suna da bukatuwa da taimakon gaggawa na abinci, sai dai yakin da ake ci gaba da yi ha hana majalisar dinkin duniyar kai musu kayan agajin.