Dakarun tsaron Yemen sun mayar da martani kan Dakarun tsaron Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i15448-dakarun_tsaron_yemen_sun_mayar_da_martani_kan_dakarun_tsaron_saudiya
Akalla Sojojin saudiya biyu ne suka hallaka a wani harin mayar da martani da Dakarun tsaron Yemen gami da na sa kai suka kai a arewacin kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:25+00:00 )
Dec 18, 2016 14:49 UTC
  • Dakarun tsaron Yemen sun mayar da martani kan Dakarun tsaron Saudiya

Akalla Sojojin saudiya biyu ne suka hallaka a wani harin mayar da martani da Dakarun tsaron Yemen gami da na sa kai suka kai a arewacin kasar

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya habarta cewa an hallaka wadannan Sojoji biyu ne a yankin Sabrin dake jihar Jauf na arewacin kasar, a yayin da Sansanin Sojojin kasar ta Yemen dake birnin Saba'a ya sanar da cewa Sojojin kasar tare da Dakarun sa kai sun samu nasarar tarwatsa tankokin yaki biyu na kasar Saudiya a yankin Najran dake kudancin kasar.

A daren jiya Assabar Jiragen kawancen Saudiya sun yi ruwan bama-bamai a yankuna daban daban na kasar daga cikin su har da jihar Sa'ada, lamarin da yayi sanadiyar shahada da kuma jikkatar fararen hula da dama, har ila yau gari na tara dake jihar Sana'a babban birnin kasar shi ma ya fuskanci lugudar wuta daga jiragen kawancen Saudiyar a daren jiya.

tun daga watan Maris din 2015, jiragen yakin kawancen masarautar Ali-sa'oud suka fara kai hare- haren wuce gona da iri kan Al'ummar kasar  ta yemen bisa da'awar dawo da halarcecciyar Gwamnati ta Abdu Rabbahu Mansur Hadi Shugaban kasar da ya yi murabus,ya zuwa yanzu hare-haren wuce gona da irin ya yi sanadiyar sahada da kuma jikkata dubu duban fararen hula a yayin da ya raba milyoyin fararen hula da mahalinsu.