Sojojin Gwamnatin Yamen Suna Ci Gaba Da Murkushe Sojojin Hayar Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i1630-sojojin_gwamnatin_yamen_suna_ci_gaba_da_murkushe_sojojin_hayar_saudiyya
Sojojin gwamnatin Yamen da dakarun sa-kai na kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi suna ci gaba da murkushe sojojin kawancen Saudiyya da suke gudanar da yaki a kasar Yamen.
(last modified 2018-08-22T06:57:54+00:00 )
Mar 03, 2016 15:50 UTC
  • Sojojin Gwamnatin Yamen Suna Ci Gaba Da Murkushe Sojojin Hayar Saudiyya

Sojojin gwamnatin Yamen da dakarun sa-kai na kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi suna ci gaba da murkushe sojojin kawancen Saudiyya da suke gudanar da yaki a kasar Yamen.

Rahotonni sun bayyana cewa; Sojojin Yamen da taimakon dakarun kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi sun samu nasarar halaka sojojin hayar masarautar Saudiyya masu tarin yawa a lardin Ma'arib tare da jikkata wasu masu yawa a yau Alhamis.

Har ila yau dakarun sa-kai na kabilun larabawan Yamen da suke goyon bayan gwamnatin kasar sun kai hare-haren kan sansanonin sojojin hayar masarautar Saudiyya a lardin Hujjah, inda suka kashe da dama daga cikin sojojin hayar tare da fatattakan wadanda suka rage.

A gefe guda kuma jiragen saman yakin masarautar Saudiyya suna ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan yankuna daban daban na kasar Yamen lamarin da ke ci gaba da lashe rayukan fararen hula da suka hada da mata da kananan yara.