Sojojin Yamen Sun Halaka Sojojin Hayar Saudiyya A Kudancin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i16708-sojojin_yamen_sun_halaka_sojojin_hayar_saudiyya_a_kudancin_kasar
Sojojin Yamen da hadin gwiwar dakarun sa-kai na Ansarullahi sun halaka sojojin hayar masarautar Saudiyya masu tarin yawa a yankin lardin Shabwa da ke kudancin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:33+00:00 )
Jan 17, 2017 04:49 UTC
  • Sojojin Yamen Sun Halaka Sojojin Hayar Saudiyya A Kudancin Kasar

Sojojin Yamen da hadin gwiwar dakarun sa-kai na Ansarullahi sun halaka sojojin hayar masarautar Saudiyya masu tarin yawa a yankin lardin Shabwa da ke kudancin kasar.

Tashar talabijin ta Almasirah ta watsa rahoton cewa: Sojojin Yamen da hadin gwiwar dakarun sa-kai na kungiyar Ansarullahi sun yi dauki ba dadi da sojojin hayar masarautar Saudiyya a yankin Asilan da ke lardin Shabwa a kudancin kasar a kokarin da sojojin hayar ke yi na shimfida ikonsu a yankin a jiya Litinin lamarin da ya janyo halakar sojojin hayar 37 tare da jikkatan wasu 23 na daban.

Har ila yau sojojin Yamen sun yi nasarar tarwatsa tankar yakin masarautar Saudiyya a yankin na Asilan a yammacin jiya Litinin tare da halaka sojojin da suke cikinta.

A wata sabuwa kuma sojojin Yamen sun harba makamai masu linzami kan wani jirgin ruwan yakin masarautar Saudiyya da ke gabar tekun Makha'u a lardin Ta'az amma babu labarin irin hasarar da harin ya haifar.