Yemen: Mutane 7 Sun yi Shahada Sanadiyyar Hare-haren Saudiyya
Rahotannin daga Kasar Yemen Sun ce mutane 7 sun yi shahada da kuma jikkata sanadiyyar harin da jirage yakin Saudiyya su ka kai a kasuwar garin al-aqiq.
Rahotannin daga Kasar Yemen Sun ce mutane 7 sun yi shahada da kuma jikkata sanadiyyar harin da jirage yakin Saudiyya su ka kai a kasuwar garin al-aqiq.
Kamfanin Dillancin Labarun Saba'a, ya nakalto cewa;Sau uku jiragen yakin na Saudiyya suna kai hari akan kasuwar al-aqiq da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 2 da kuma jikkatar wasu biyar.
Bugu da kari, jiragen yakin na Saudiyyar sun kai wasu hare-haren a yankin Maran da ke kusa da Haydan, da ya yi sanadin shahadar wasu mutanen 7 da jikkata wasu da dama.
Kusan shekaru 2 kenan da Saudiyya ta shelanta yaki a kan kasar Yemen wanda kawo ya zuwa yanzu sun ci dubban rayuka da jikata wasu. Majalisar Dinkin Duniya ta ce; Mutane 10,000 ne su ka rasu sanadiyyar yakin na saudiyya.