Yemen: Yankin Sa'ada Yana Cikin Mummunan Hali.
Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama Sun Sanar da cewa; Yankin Sa'adah ya rasa muhimman ginshikan bukatun rayuwa, saboda hare-haren Saudiyya.
Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama Sun Sanar da cewa; Yankin Sa'adah ya rasa muhimman ginshikan bukatun rayuwa, saboda hare-haren Saudiyya.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasar Yemen sun sanar a jiya alhamis cewa;Daga fara kai hare-haren Saudiyya a cikin Yemen, zuwa yanzu, adadin mutanen da aka kashe a cikin gundumar Sa'adha kadai sun kai 5000.
Bugu da kari, hare-haren na Saudiyya sun rusa duk wani abu mai amfani ga al'umma a cikin gundumar da su ka hada da asibitoci da cibiyoyin samar da wutar lantarki da kuma ruwan sha.
A cikin watan Maris na 2015 ne dai Saudiyya bisa cikakken goyon baya da taimakon Amurka da Birtaniya su ka fara kai wa Yamen da al'ummarta hare-hare, wanda kawo ta zuwa yanzu ya ci rayukan mutane 10,000 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar.