Ci gaba da kai hare-haren ta'addanci kan Al'ummar kasar Yemen
Jiragen yakin Kawancen Saudiya sun kai hare hare ta sama a yankuna da dama na kasar Yemen
Kafar watsa labaran Almu'utamar ta habarta cewa a daren jiya Assabar da kuma safiyar yau Lahadi Jiragen yakin kawancen Saudiya sun yi lugudar wuta har so goma a yankuna daban daban na garin Sarwah dake jihar Ma'arib na tsakiyar kasar Yemen, harin da ya janyo asara mai yawa ga gidaje da kuma gonakin Noma na fararen hula.
A yankin Sana'a fadar milkin kasar, jiragen yakin kawancen Saudiya sun kai hare hare da dama kan gidajen fararen hula na anguwanin Sanhan da Bani Bahlul, ya zuwa yanzu babu wani rahoto da aka sanar dangane da asarar rayuka ko Duniya da wadannan hare-hare ya janyo.
A bangare guda, Tashar telbijin din Al-Alam ta habarta cewa Sojoji da Dakarun sa kai na kasar ta Yemen sun tarwatsa wata motar soja mai sulke mallaki kawance saudiya, lamarin da ya yi sanadiyar hallakar Sojojin hayar Saudiyan kimanin 23.
A nata bangare Tashar telbijin din Almayadin ta habarta cewa Sojojin Yemen din sun halba rokoki da dama a matattarar Sojojin Saudiyar dake yankin Asir na Kudancin kasar, a matsayin mayar da martani.