Saudiya ta kori duban Ma'aikata yan kasar Pakistan
(last modified Fri, 10 Feb 2017 17:46:16 GMT )
Feb 10, 2017 17:46 UTC
  • Saudiya ta kori duban Ma'aikata yan kasar Pakistan

Mahukuntan Saudiya sun kori duban Ma'aikata 'yan kasar Pakistan kan zarkin su nada alaka da hare-haren ta'addanci

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya habarta cewa cikin watani hudu da suka gabata kimanin Ma'aikata 'yan kasar Pakistan dubu 39 ne aka mayar da su kasar kan da'awar cewa su nada hanu a hare-haren ta'addanci da ake kaiwa cikin kasar.

A baya ma Mahukuntan Saudiyan sun mayar da 'yan kasar Pakistan kimanin 50 zuwa kasar ba tare da bayyana dalilin su na yin hakan ba.

Kasar Saudiyan na fuskantan matsin tattalin arziki, sanadiyar faduwar farashin Man fetur a Duniya da kuma kudaden da take kashewa a yakin wuce gona da irin da take kaiwa kan Al'ummar kasar Yemen, wanda masana ke ganin cewa wannan shi ne dalilin da ya sanya mahukuntan na Saudiyar ke korar Ma'aikata na kasashe waje daga cikin kasar.