jerin gwanon Al'ummar kasar Yemen gaban Ofishin MDD
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i17890-jerin_gwanon_al'ummar_kasar_yemen_gaban_ofishin_mdd
A karo na 61 cikin shekararu biyu, Al'ummar kasar Yemen sun taron gaban MDD inda suka bukaci Majalisar ta dakatar da Saudiyar kan hare-haren wuce gona da iri da take kai musu.
(last modified 2018-08-22T06:59:43+00:00 )
Feb 21, 2017 08:16 UTC
  • jerin gwanon Al'ummar kasar Yemen gaban Ofishin MDD

A karo na 61 cikin shekararu biyu, Al'ummar kasar Yemen sun taron gaban MDD inda suka bukaci Majalisar ta dakatar da Saudiyar kan hare-haren wuce gona da iri da take kai musu.

Mazauna birnin Sana'a fadar mikin kasar Yemen, da na Ta'az dake kudancin kasar sun yin tsintsirundu gaban Ofishin MDD a wannan talata, inda suka bayyana cewa hare-haren wuce gona da iri da kawancen Saudiya ke kaiwa a babu Mandib, tsibirin Maha dake kudu da kuma kudu maso gabashin kasar ya yi sanadiyar raba da fararen hula sama da dubu 50 da mahalinsu.

Bayan yin alawadai da wannan ta'addanci, Al'ummar kasar ta Yemen ta turwa Kwamitin tsaron MDD sako ta hanyar ofishin MDD na Kasar inda suka bukaci da a dakatar da hare-haren wuce gona da irin da ake kaiwa kan Al'ummar kasar, takunkumin da aka sanyawa kasar tare da kara yawan taimakon da ake kaiwa cikin kasar domin karin yawan mabukata.

A yayin ganawarsu da Sofia Sulemanu wakilin MDD a kasar sun bayyana masa irin matsanancin halin rayuwa da kuma irin yawan Mutanan da aka kashe sanadiyar hare-haren wuce gona da irin da kawancen Saudiya ke kaiwa cikin kasar.