Iraki : Da'esh Ta Shiga Tsaka- Mai- Wuya A Mosul
Dakarun Iraki sun yi nasara mamaye duk hanyoyin motoci dake kaiwa Birnion Mosul daga yammaci, wanda kuma ya zama babban kalubale ga kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh a babban sansanin na ta dake Iraki.
A cewar wakilin Amurka a kawacen yaki da kungiyar Da'esh kungiyar ta shiga tsaka mai wuya a halijn yanzu cikin wanna yakin.
A cikin daren jiya ne bataliya ta 9 ta rundinar sojin kasar Iraki dake yankin Badouch a arewa maso yammacin Mosul ta karbe hanya ta karshe ta birnin wanda shi ne na biyu mafi girma a kasar.
hakan kuma a cewar Mista Brett McGurk dukkan mayakan na Da'esh zasu halaka.
kafin hakan wasu alkaluma da jami'an Amurka suka fitar sun kiyasta mayakan na Da'esh 2,500 dake a yammacin birnin na Mosul da kuma Tal-Afar dake yammaci.
A watan Yuni na shekara 2014 ne kungiyar Da'esh ko kuma IS ta kwace yankin na Mosul wanda ya bata damar mamaye yankuna da dama a yammaci da kuma arewacin kasar ta Iraki.