Yahudawan Sahayoniyya 'Yan Kaka Gida Sun Killace Wani Yankin Masallacin Aksa
Mar 13, 2017 07:23 UTC
Tsagerun yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida sun sake daukan matakin mamaye wani yankin Masallacin Aksa da ke birnin Qudus.
A ci gaba da keta hurumin Masallacin Aksa da ke birnin Qudus a Palasdinu, wasu gungun tsagerun yahudawan sahayoniyya da suke samun kariya daga sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun mamaye wani yanki na Masallacin Aksa daga bangaren kofar Almagharibah a safiyar yau Litinin.
A kokarin da suke yi na tunzura Palasdinawa; Tsegerun yahudawan sahayoniyyan sun dauki matakin mamaye bangaren Masallacin na Aksa ne da sunan gudanar da ayyukan ibadunsu a wajaje masu tsarki lamarin da ke kai ga bullar tarzoma a Masallacin na Aksa.
Tags