Wasu Bama-Bamai Sun Tashi A Birnin Bagadaza Na Kasar Iraki
Wasu bama-bamai sun tashi a yankin arewa da kuma yammacin birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki a yau Laraba.
Majiyar 'yan sandan Iraki ta sanar da cewa: Wani bom ya tashi a kan hanya a yankin Sha'ab dake arewacin birnin Bagadaza a yau Laraba, inda ya jikkata mutum guda. yayin da wani bom din na daban ta tarwatse a kusa da wata kasuwa da ke yankin Abu-Ghuraib a yammacin birnin na Bagadaza lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwan mutum guda tare da jikkata wasu biyar na daban.
Majiyar 'yan sandan ta kara da cewa: Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a yankin kudancin birnin na Bagadaza a jiya Talata, inda ta lashe ryukan fararen hula 13 tare da jikkata wasu 31 na daban.
Kasashen Iraki da Siriya suna fama da matsalolin tsaro tun bayan da aka jabge 'yan ta'addan kasa da kasa a cikinsu da nufiun tarwatsa kasashen kuma kasar Amurka da kawayenta musamman na kasashen Larabawa da Turkiyya suke tllafawa 'yan ta'addan.