Bom Ya Kashe Mutane 22 A Pakistan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18996-bom_ya_kashe_mutane_22_a_pakistan
Rahotanni daga pakistan na cewa mutane akalla 22 ne suka rasa rayukansu kana wasu 57 na daban suka jikkata a wani harin bom da aka kai da mota a wata kasuwa dake arewa maso yammacin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:29:53+00:00 )
Mar 31, 2017 09:34 UTC
  • Bom Ya Kashe Mutane 22 A Pakistan

Rahotanni daga pakistan na cewa mutane akalla 22 ne suka rasa rayukansu kana wasu 57 na daban suka jikkata a wani harin bom da aka kai da mota a wata kasuwa dake arewa maso yammacin kasar.

Bam din ya tarwatse ne a wata kasuwa da ke yankin na mabiya mazahabar Shi'a a wannan Jumma'a.

galibin dai wadanda harin ya rutsa mata ne da kuma yara kamar yadda wani likitan tiyata ya shidawa kamfanin dilnacin labaren AFP.

Tuni dai wani reshen kungiyar Taliban mai suna Jamaat-ul-Ahrar (JuA) ya yi ikirarin daukar alhakin kai harin.