Sojojin Iraki Sun Kashe Jagoran Da'esh Na Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19056-sojojin_iraki_sun_kashe_jagoran_da'esh_na_biyu
Rundinar sojin Iraki ta sanar da kashe jagora na biyu na kungiyar IS (Da'esh) wato Ayad Hamid al-Jumaili, yayin wani farmaki da sojojin kasar suka kai kwanan baya a yankunan yammacin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:29:54+00:00 )
Apr 02, 2017 10:16 UTC
  • Sojojin Iraki Sun Kashe Jagoran Da'esh Na Biyu

Rundinar sojin Iraki ta sanar da kashe jagora na biyu na kungiyar IS (Da'esh) wato Ayad Hamid al-Jumaili, yayin wani farmaki da sojojin kasar suka kai kwanan baya a yankunan yammacin kasar.

Bayanai sun nuna cewa mutumin da aka kashe, ya zama jagora na biyu na IS, biyo bayan Abu Bakr al-Baghdadi.

Baya ga Jumaili din, akwai sauran wasu jagororin kungiyar ta IS wadanda aka kashe a yayin luguden wutan.

A halin yanzu, sojojin gwamnatin Iraki na kokarin kwace ikon birnin Mosul daga hannun IS.

Idan ana tuni a karshen watan Maris, hukumar leken asirin kasar Iraki ta ce, sojojin saman kasar sun yi luguden wuta kan maboyar 'yan ta'addan IS guda uku a garin Ba'aj dake kan iyakar kasar da Siriya, inda suka hallaka kusan 200 daga cikinsu, wadanda suka shigo Iraki daga kasar Siriyar.