Kokarin Kasashen Yamma Na Tunzura MDD Kan Gwamnatin Syria Ya Cutura
Kokarin da kasashen yamma suka yi na tunzura Majalisar Dinkin Duniya (MDD) kan gwamnatin kasar Syria dangane da zargin amfani da makaman guba a kan mutanen Khan Shaikhun bai kai ga nasara ba.
Tashar television ta AL-Alam a nan Tehran ta nakalto mataimakin jakadan kasar Rasha a majalisar dinkin duniya Lavrov Sofrunkuf yana fadawa komitin tsaro na MDD a zaman gaggawa da ya gudanar a kan wannan batun a jiya Laraba, kan cewa yan ta'adda a kasar Syria tarae da masu goyon bayansu sun so su yi amfani da batun hari da makaman guba a kan garin Khan Shaikun na lardin Idlib a kasar Syria don tunzura MDD ta dauki matakin soje kan gwamnatin kasar Syria, amma hakarsu bata cimma ruwa ba.
Manzir Manzir mataimakin jakadan kasar Syria a Majalisar Dinkin Duniya, shi ma a yayin da yake kare gwamnatin kasar Syria kan tuhumce tuhumcen kasashen Amurka, Britania da kuma Faransa kan wannan batun ya ce gwamnatin kasar Syria ta gabatarwa MDD kwakkwaran shaida a cikin wasiku 90 da ta aikawa majalisar a baya, kan cewa yan ta'adda suna amfani da makaman guba a yankunan da suke iko da su sannan suna shigo da makaman guban ne daga kasar Turkia.
A ranar Asabar da ta gabata ce mutane kimani 100 suka rasa rayukansu a yayin da wasu 400 suka ji rauni a hari da makaman guba da aka kai a garin Khan Shaikhun na kasar Syria wanda yake karkashin ikon yan ta'adda.