Dakarun Kasar Yamen Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanin Sojin Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19374-dakarun_kasar_yamen_sun_yi_luguden_wuta_kan_sansanin_sojin_saudiyya
Sojojin Yamen da dakarun sa- kai na kasar sun yi luguden wuta kan sansanin sojin Saudiyya da ke lardin Jizan na kasar ta Saudiyya.
(last modified 2018-08-22T06:59:57+00:00 )
Apr 12, 2017 07:24 UTC
  • Dakarun Kasar Yamen Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanin Sojin Saudiyya

Sojojin Yamen da dakarun sa- kai na kasar sun yi luguden wuta kan sansanin sojin Saudiyya da ke lardin Jizan na kasar ta Saudiyya.

Rundunar sojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar a yau Laraba sun yi luguden wuta kan sansanin sojin masarautar Saudiyya da ke lardin Jizan a kudancin kasar Saudiyya a matsayin maida martani kan harin da sojojin Saudiyya suka kaddamar kan lardin Sa'adah da ke arewacin kasar Yamen.

Rahotonni sun bayyana cewa: Sojin Yamen da dakarun sa-kan sun yi nasarar tarwatsa tankokin yaki, motoci masu silke, makamai masu linzami da sauransu da suke sansanin na sojojin Saudiyya lamarin da ya firgita mahukuntan Saudiyya.

Har ila yau sojojin Yamen da dakarun sa- kai na kasar sun kai wasu jerin hare-haren daukan fansa da makamai masu linzami kan sansanin sojin Saudiyya da na kawayenta 'yan mamaya a yankin Al-Mukha da ke yammacin Saudiyya, inda hare-haren suka yi sanadiyyar halakar sojoji masu tarin yawa.