An 'Yanto Kashi 83% Na Garin Mosil
(last modified Thu, 27 Apr 2017 18:03:26 GMT )
Apr 27, 2017 18:03 UTC
  • An 'Yanto Kashi 83% Na Garin Mosil

Kakakin Ma'aikatar cikin gidan kasar Iraki ya ce bayan 'yanto bangaren gabashin Mosil kashi 83% na Mosil an tsarkake shi daga hanun 'yan ta'addar ISIS

A cikin wata sanarwa da Kakakin Ma'aikatar cikin gidan kasar Iraki Sa'ad Mu'in ya fitar a wannan Alkhamis ya ce bayan fatattakar 'yan ta'addar IS a kauyuka da dama na yankin Alhadar dake yammacin Mosil, Komandan rundunar hadin gwiwa na 'yanto garin Mosil din ya bukaci taimakon gaggauwa  domin 'yanto sauren yankunan dake suka rage a hanun 'yan ta'addar IS.

Yayin da yake ishara kan rawar da jami'an tsaron kasar ke takawa wajen bayar da kariya ga fararen hula a Mosil, Mu'in ya ce Ma'aikatar cikin gidan kasar na aiki kafa da kafa tare da fararen hula wajen tsegunta mata 'yan ta'addar dake kokarin sajewa a tsakanin fararen hula.

Yayin da yake ishara kan irin kashin da Komondojin 'yan ta'adda suka sha a Iraki da Siriya, Jami'in ya ce faduwar Komondojin 'yan ta'adda na a matsayin rushewar inji a Mota to kaka babu yadda za a yi 'yan ta'addar su iya barkata wata tsiya a nan gaba, bayan Shugaban kungiyar Ta IS Abubakar Bagdadi ba za a samu wani shugaba da zai mayar gurbinsa ba a kasar ta Iraki.