Taliban Ta Shelanta Farmaki Kan Dadarun Ketare A Afganistan
Kungiyar Taliban a kasar Afganistan ta shelanta wani farmaki mai suna ''Operation Mansouri'' kan dakarun kasashen waje dake kasar.
A sanarwar data fitar Tabilan ta ce shirin mai taken dake dauke da sunan tsohon jagoranta babbar manufarsa shi ne kai hare-hare kan dakaru, cibiyoyin soji, da na leken asiri kasashen waje har ma da jami'an tsaron kasar ta Afganistan.
Saidai tuni gwamnatin kasar ta Afganistan ta bakin kakakin ministan cikin gidanta, Najib Danish ta yi fatali da wannan barazana tana mai cewa ba yau ta saba jin hakan ba daga kungiyar.
Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan kazamin harin da kungiyar taliban din ta kai kan wani barikin sojin kasar wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Afganistan din 135.