Mutanen Kasar Yemen Na Kara Fadawa Cikin Mawuyacin Hali Saboda Yaki
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Kasashe Su Taimakawa Al'ummar Yemen Da Su ke cikin Mawuyacin hali.
Jami'i mai kula da ayyukan agaji na majalisar dinkin duniya Jamie McGoldrick ya yi kira ga kasashen da su ke bada taimako da tallafawa al'ummar Kasar Yemen domin cika alkawalinsu akan Yemen din.
Jami'in ya ci gaba da cewa; Yanayin al'ummar kasar ta Yemen ya kara muni sosai, tare da nuna damuwarsa akan rashin magani da kayan aiki na likitanci a cikin asibitoci.
Har ila yau, ya yi kira da a bude dukkanin tasoshin jiragen ruwan kasar ta Yemen domin shigar da kayan agaji cikin gaggawa.
An shiga shekara ta uku kenan ajere da Saudiyya ta shelanta yaki akan Yemen da al'ummarta, da kawo ya zuwa yanzu ya ci rayuka masu yawa.