Mutane 115 Suka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Cutar Kwalera A Yemen
May 14, 2017 13:51 UTC
Cutar Cholera ta lashe rayukan mutane 115 a kasar Yemen sannan wasu dubban kuma suna fama da cutar tun lokacin barkewansa a cikin watan Afrilun da ya gabata
Majiyar kungiyar bada agaji ta red cross a kasar ta shaifawa Presstv kan cewa annobar ya ta kashe mutane 115 daga ranar 27 ga watan Afrilu zuwa 13 ga watan mayu da muke ciki.
Directa na kungiyar ta red cross a kasar yemen ,Dominik Stillhart ya ce annobar ta shafi jihohi fiye da 10 a kasar, kuma a halin yanzu asbotocin da suka rage a cike suke da marasa lafuya. wasu a waje suke kwana wasu kuma suna cikin motocinsu don rashin wuri a asibitocin da suka rage
Tags