Sabon Kawancen Amurka, Saudiyyah, Isar'ila, Domin Yaki Da Iran
Bayan gama ziyarar da ya kai a birnin Riyadh fadar masarautar Saudiyya, tare da gabatar da jawabi ga wasu shugabannin larabawa da na wasu kasashen musulmi, Donald Trump kai tsaye ya wuce zuwa Isra'ila.
Ziyarar tasa a Isra'ila ba ta da wani banbamci da wadda ya kai a Saudiyya a siyasance, domin kuwa tana a matsayin ci gaba ne na abin da suka cimma matsaya a kansa tare da sarakunan Saudiyya, wato hada karfi da karfe a tsakaninsu domin yaki da Iran, inda bayan isarsa Isra'ila, Trump ya tabbatar da cewa wannan kawance ne na Amurka da Saudiyya da Isra'ila domin yaki da kasar Iran, wadda ta zama babban karfen kafa da ke kawo tarnaki ga manufofinsu a yankin gabas ta tsakiya.
Tun da Trump ya saka kafarsa a cikin Saudiyya dai har ya bar kasar bai yi magana a kan mulkin dimukradiyya ko kare hakkokin bil adama ba, kamar yadda bai yi maganar harin 11 ga watan Satumba da aka kaiwa Amurka ba, haka nan kuma bai yi magana a kan kawo karshen zaluncin da Palastinawa suke fuskanta a hannun yahudawan Isra'ila ko kuma wajabcin kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta ba.
To sai dai a nasa bangaren shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani a zaman farko da manema labarai da ya gudanar a jiya a birnin Tehran, ya mayar da martani a kan zaman da Amurka da Saudiyya gami da 'yan koransu suka gudanar a Riyadh, zaman da ya ce na jeka na yi ka ne wanda ba shi da wata kima.
Shugaba Rauhani ya ce Trump ya shigo yankin gabas ta tsakiya ne a daidai lokacin da ake gudanar da zabe a Iran, inda mutane suke kada kuri'a a cikin 'yanci domin zabar abin da suke so, a daidai lokacin da yake ziyara a kasar da al'ummarta ba su taba ganin akwatin zabe ba, Rauhani ya ce yana baiwa masu rike da madafun iko a saudiyya shawara, maimakon kwasar biliyoyin dalolin talakawa da suke yi suna ta mika wa Amurka da sunan za a ba su makamai domin su kare kansu daga harin Iran, da zai fi kyau su mayar da hankali wajen gyara tsarin kasarsu ta yadda mutane za su ji su ma a na yi da su, wanda hakan ita ce babbar matsalar mahukuntan Saudiyya da suka kasa ganewa, shi yasa a kullum suke cikin tsoro da damuwa, matsalarsu ba Iran ba ce, matsalarsu tana nan cikin gida tattare da tsarinsu na mulkin mulukiyya, wanda talaka ba shi da rabo a cikinsa.
Rauhani ya kara da cewa; Amurka tana yi wa Saudiyya wayau tana karbe mata kudade tana firgita ta da Iran, ya ce Saudiyyah ce ke bukatar sayen makami, Iran kuwa Allah ya hore mata fasahar da za ta kera makamin da take bukata da kanta, wanda kuma wadannan makamai na kare kai ne da tabbatar da tsaro a yankin gabas ta tsakiya baki daya, domin kuwa Iran ta taimaka wa kasashen da suke fama da matsalar ta'addanci da aka haifar musu, kuma sun ga tasirin taimakon nata, yayin da su kuma masu zargin Iran, duniya tana ga irin rawar da suke takawa wajen daukar nauyin ta'addanci da sunan addini, a Syria, Iraki, Libya, Afghanistan, Yemen, da sauransu.
Rauhani ya kirayi Trump da ma dukkanin masu yi masa amshin shata da su kwana da sanin cewa, Amurka ko wata kasa ta duniya, ba su da hurumin da Iran za ta nemi izini daga gare su domin gwajin makamanta, ba ma maganar karbar izini ba, ba su da ma hurumin da zata sanar da su.
Da dama daga cikin masana suna ganin cewa, babbar manufar wannan yawo da Trump ke yi a gabas ta tsakiya dai ita ce tabbatar da tsaron yahudawan Isra'ila, domin kuwa kada kugen yakin da ya yi a kan Iran daga birnin Riyadh ba manufarsa kare Saudiyya ko wata kasa daga cikin kasashen larabawa ba ne, manufar ita ce kare Isra'ila wadda a kullum take kallon Iran a matsayin babbar barazana a gare ta, kamar yadda hatta makudan kudaden da Amurka take karba daga hannun Saudiyya da wasu larabawan yankin irinsu UAE, Bahrain, da Qatar, duk mafi yawansu za su tafi ne wajen karfafa tsaron Isra'ila da kuma kara danne al'ummar Palastinu marassa kariya, kamar yadda kuma wasu daga cikin makaman da wadannan gwamnatocin kasashen larabawa suke saye na biliyoyin daloli daga Amurka, suna tafiya ne a hannun kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Al-qaeda, ISIS da sauransu, wadanda ake amfani da su wajen hare-haren ta'addanci da sunan jihadi a cikin kasashen larabawa irin su Syria da Iraki da Libya da sunan jihadi, kamar yadda kuma wasu daga cikin makaman da Saudiyya ta kulla cinikin sayen su daga Amurka yayin ziyarar Trump a Riyadh, Saudiyya za ta yi amfani da su ne wajen kai hare-hare a kan al'ummar musulmi larabawa na kasar Yemen.
To sai dai wani abu da masana harkokin siyasa na duniya suka yi imani da shi, shi ne cewa, dukkanin kasashen larabawan da Amurka take amfani da su domin cimma manufofinta ayankin gabas ta tsakiya, magana ce kawai ta lokacin da Amurka take da maslaha da su, da zaran maslarta ta kare, tabbas za ta yi watsin shara da su, kamar yadda ta yi hakan a kan takwarorinsu da dama suka gabata.