IS Ta Dauki Alhakin Kai Harin Indonusiya
May 26, 2017 08:19 UTC
Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kai tagwayen hare haren da sukayi sanadion mutuwar 'yan sanda uku a birnin Jakarta na kasar Indonusiya.
Da yammacin ranar Laraba data gabate ce wasu 'yan kunar bakin wake biyu suka tayar da boma-bomansu a kusa da wata tashar manyan motoci ta Kampung Melayu dake a daya daga cikin mayan unguwani na babban birnin kasar.
Masu sharhi kan lamuran yau da kullun sun ce sanarwar ta IS tana da sahihanci kasancewar kungiyar Jamaah Ansharut Daulah (JAD) a kasar ta Indonesiya ta yi mubayi'a ga kungiyar 'yan ta'addan ta IS.
'Yan sanda a kasar dai sun ce sun cafke mutane uku da ake zargi da hannu a jerin hare-haren.
Tags