Pakistan Ta Sake Bude Iyakarta Da Afganistan
(last modified Sat, 27 May 2017 15:27:54 GMT )
May 27, 2017 15:27 UTC
  • Pakistan Ta Sake Bude Iyakarta Da Afganistan

Hukumomi a Pakistan sun sanar da sake bude iyakar kasar da Afganistan a dalilin watan Azumin Ramadana, makwanni kadan bayan arangamar data wakana tsakanin sojojin kasashen biyu.

Yankin Chaman dake iyaka tsakanin kasashen Pakistan da Afaganistan na da matukar mahimmacin ga kasashen biyu ta fuskar kasuwanci.

A farkon watan Mayu ne aka rufe iyakar lokacin sojojin Afaganistan suka bude wuta kan wata tawagar masu kidayar jama'a na Pakistan inda suka kashe akalla fararen hula takwas da kuma wani adadi da ba'a bayyana ba na sojoji.

Hukumomin Aganistan dai sun zargi ma'aikatan na Pakistan da shiga yankin domin kidayar jama'a dake rayuwa a wurin.

A wani labari dai rundinar sojin Pakistan ta ce ta bude iyakar ne bisa dalilai na jin kai, sannan ba zata jirewa duk wani yunkuri na tsokana ba.

Ko baya ga rikicin iayak na tsakanin kasashen biyu, kasar Afganistan na zargin gwamnatin Pakistan da goyan bayan 'yan taliban na Afganistan, a yayin da ita ma gwamnatin Pakistan ke zargin Afaganistan da baiuwa mayakn dake kai hari cikin kasarta mafaka.