MDD : Yemen Na Fuskantar Babbar Barazanar Yunwa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i20874-mdd_yemen_na_fuskantar_babbar_barazanar_yunwa
MDD ta nuna damuwa matuka akan halin da ake ciki kan matsalar kamamcin abunci a kasar Yemen.
(last modified 2018-08-22T07:00:11+00:00 )
May 31, 2017 01:21 UTC
  • MDD : Yemen Na Fuskantar Babbar Barazanar Yunwa

MDD ta nuna damuwa matuka akan halin da ake ciki kan matsalar kamamcin abunci a kasar Yemen.

Mukadashin sakatare janar na MDD mai kula da ayyukan jin kai, Stephen O'Brien ya bayyana a zauren kwamitin tsaro na MDD da matsalar wacce ta kasance mafi muni a duniya.

Wakilin MDD kan rikicin kasar Yemen,  Ismaïl Ould Cheikh Ahmed ya bayyana a zauren kwamitin tsaro na MDD cewa yaki da ake fama da shi a yemen ya ruguza kashi 4% na muhallai jama'a a yankin Mokha.

Kimanin Miliyan bakwai nan al'ummar Yemen na fama da yunwa a yayin da kuma cutar kwalera a kashe mutane 500 a wannan kasa. 

Mafi yawa daga cikin wadanda wannan iftila'in yafi shafa yara kanana ne. 

MDD ta bukaci bangarorin dake rikici a kasar dasu gaggauta samar da hanyoyin da zasu kai ga isar da kayan agaji ga mabukata.