Cutar Kwakera Ta Kashe Mutane 789 A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i21146-cutar_kwakera_ta_kashe_mutane_789_a_yemen
Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane sama da dubu dari ne suka kamu da cutar amai da gudawa ko kuma kwalera a kasar Yemen.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jun 08, 2017 16:12 UTC
  • Cutar Kwakera Ta Kashe Mutane 789 A Yemen

Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane sama da dubu dari ne suka kamu da cutar amai da gudawa ko kuma kwalera a kasar Yemen.

Kawo yanzu dai mutane 789 ne suka rasa rayukansu sanadin cutar mai saurin yaduwa tun bayan bullatar a tsakiyar watan Afrilu daya gabata a wannan kasa ta Yemen mai fama da rikici, kamar yadda wani kakakin hukumar, Tarik Jasarevic ya bayyanawa kamfanbin dilancin labaren AFP.

A rahoton data fitar yau Alhamis hukumar ta WHO ko kuma OMS ta ce mutane dubu dari da daya, da dari takwas da ashirin ne suka kamu da cutar inda 789 suka rasu a cikin yankuna 19 a kasar.

kafin hakan dai wani rahoto da kungiyar agaji ta oxfem  ta fitar ya nuna cewa mutun guda ne cutar ta kwalera ke kashewa a cikin ko wacce awa guda a kasar ta Yemen.

Tunda farko dama hukumar ta nuna matukar damuwarta akan halinda ake ciki dangane da yaduwar cutar ta kwalera a kasar ta Yemen, inda ta bukaci agajin gaggawa don dakile cutar musamen a yankuna masu wahalar shiga.

Hukumar ta ce muddun dai ba'a dauki matakai ba cutar za ta iya shafar mutane kusan dubu dari biyu da hamsin a cikin wattani shida masu zuwa.