Rasha Ta Ce Akwai Yiwuwar An Kashe Albaghdadi
(last modified Sat, 17 Jun 2017 07:00:04 GMT )
Jun 17, 2017 07:00 UTC
  • Rasha Ta Ce Akwai Yiwuwar An Kashe Albaghdadi

Ma’ikatar harkokin wajen Rasha ta ce akwai yiwuwar an kashe jagoran ‘yan ta’addan ISIS Abubakar Baghdadi a wani hari a kusa da Raqqa.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar tsaron kasar Rashe ta ce akwai yiwuwar an halaka jagoran kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh Abubakar Baghdadi a wani hari da aka kai a kusa da Raqqa.

Bayanin ya ce a ranar 28 ga watan Mayun da ya gabata, Rasha ta kai wani hari da jirgi maras matuki a wani wuri a kusa da birnin raqqa da ke hannun ‘yan ta’addan takfiriyyah na ISIS, bayan samun bayanai na sirri a kan wani zama da 'yan ta'adda suke gudanarwa.

Ma’aikatar tsaron ta Rasha ta ce ‘yan ta’addan suna tattaunawa ne a kan shirin ficewa daga Raqqa, inda jirgin na Rasha ya tarwatsa wurin da suke gudanar da zaman, an kuma kashe mayakan ISIS 330 a wurin, da suka hada har da manyan kwamandojin kungiyar guda 30 da ake kyautata zaton cewa har da Abubakar Baghdadi a cikinsu.

A nata bangaren Amurka ta bayyana cewa ba za ta yi saurin amincewa da wannan bayani na Rasha dangane da halaka Abubakar Baghdadi ba.