Haidar Abadi Ya Sanar Da Kawo Karshen Mulkin ISIS A Iraki
Firayi Ministan Iraki Haidar Abadi ya sanar da kawo karshen mulkin 'yan ta'adda a kasar Iraki baki daya, bayan kawo karshensu a Mausul.
Tashar talabijin ta Alirakiyya ta bayyar da rahoton cewa, Abadi ya fadi yau cewa gwamnatin ta'addanci da sunan musulunci da 'yan ta'addan takfiriyyah na Daesh suka kafa a wasu yankunan Iraki ta zo karshe.
A yau dakarun Iraki sun shiga cikin majami'ar Sa'a da kuma masallacin Umar Aswad, wadanda su ne muhimman wuraren da suka rage a hannun 'yan ta'addan ISIS a garin Mausul.
Abdulamir Rashid Yarallah babban jami'in rundunar kwato lardin Nainawa daga hannun 'yan ta'addan takfiriyya ya bayyana cewa, sun gama karya lagon kungiyar a Mausul, domin kuwa majamia'ar Sa'a da kuma masallacin Umar Aswad a halin yanzu na hannun dakarun Iraki.
Ya kara da cewa yanzu haka sauran 'yan ta'adda da suka rage sun tarwatse, kuma ana ci gaba da bin sawunsu domin tabbatar da cewa babu ko daya daga cikin 'yan ta'addan da ya yi saura a cikin Mausul da ma lardin na Nainawa baki daya.
Tun a cikin shekara ta 2014 ce Ibrahim Samirra'i wanda ake yi wa lakabi da Abubakar Albaghdadi, tare da taimakon wasu daga cikin kasahen larabawa, ya jagoranci dubban mayakan 'yan ta'addan takfiriyya daga kasashen duniya daban-daban, wajen mamaye wasu yankuna na kasar Iraki, da sunan kafa daular Islama.