Syria: An Kashe Kwamandojin "Da'esh" Masu Yawa
Tashar Telbijin din "Russia Today" ta gwamnatin Rasha ta ce; Harin da sojojin Syria su ka kai a Dar'a ya yi sanadin mutuwar kwamandojin Da'esh 10.
Tashar Telbijin din "Russia Today" ta gwamnatin Rasha ta ce; Harin da sojojin Syria su ka kai a Dar'a ya yi sanadin mutuwar kwamandojin Da'esh 10.
Rahoton ya ci gaba da cewa An kashe kwamandojin 'yan ta'addar ne a daidai lokacin da sojojin na Syria su ka 'yantar da wasu yankuna a gundumar Hums.
A gefe daya, sojojin na Syria sun gano wasu hanyoyin karkashin kasa da aka haka a gefen birnin Damascuss, domin shigar da makamai.
A gabacin garin Halab da ke arewacin kasar ta Syria, sojojin gwamnati sun dakile hare-haren kungiyar Da'esh a garuruwan Rasm Askar, Shuraimah da Jadidah.