Kungiyar ISIS Ta Kona Mutane 12 Lokaci Guda A Iraki
A cikin wani sabon ta'addanci da kungiyar ISIS ta aiwatar a kasar Iraki, ta kona fararen 12 a garin Hawija dake kudu maso yammacin jihar Karkuk.
Bayan kashin da ta sha a hanun jami'an tsaron kasar Iraki gami da Dakarun sa kai na Hashadu Sha'abi musaman ma a jihar arewacin Nainuwa, kungiyar ta'addancin IS ta yi karkuwa da fararen hula sama da 900 a garin Hawija, a yayin da wasu 12 daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su,suka yi yunkurin gudu, mayakan ISIS din sun sanya su cikin keji guda sannan suka sanya musu wuta har saida suka kone kurmus.
Tun a shekarar 2014 ne kungiyar ISIS din dake samun goyon bayan kudi daga kasar Saudiya da kuma na Soja daga kasashen Amurka da Turkiya suka kai farmaki kasar Iraki tare da mamaye wani bangaren kasar mai fadi daga cikin yankunan Arewa da yammacin kasar, tare da aiwatar da ta'addanci a kan fararen hula.
A halin da ake ciki Dakarun tsaron kasar sun tsarkake mafi yawa daga cikin yankunan da aka mamaye, kuma na dab da kawo karshen 'yan ta'addar daga cikin kasar baki daya.