Sojojin Gwamnatin Syria Sun Ragargaza Wasu Sansanonin 'Yan Ta'addan ISIS
(last modified Wed, 12 Jul 2017 18:01:47 GMT )
Jul 12, 2017 18:01 UTC
  • Sojojin Gwamnatin Syria Sun Ragargaza Wasu Sansanonin 'Yan Ta'addan ISIS

A ci gaba da kara nausawa da dakarun Syria suke yia cikin yankunan da ke karkashin ikon 'yan ta'addan ISIS, a jiya dakarun na Syria sun ragargaza wasu sansanonin 'yan ta'addana cikin yankin Badiyyah da ke arewacin kasar.

Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, sojojin an Syria tare da mayakan kungiyar Hizbullah sun samu damar rusa sansanoni 'yan ta'addan takfiriyya da dama a cikin gundumar Suwaida a jiya, tare da kwace yannkuna daga hannun 'yan ta'adda da tazararsu ta kai kilo mita 80.

Janar Imad Iskandar babban kwamandan bataliyar yankin Suwaida na Syria ya bayyana cewa, 'yan ta'addan suna cikin mawuyacin hali, inda suka shiga cikin firgici sakamakon kashin da suke sha a hannun dakarun Syria da kawayensu, wanda kuam a cewarsa rikicin da ya kunno kai tsakanin Saudiyya da Qatar ya taimaka matuka wajen karya lagon 'yan ta'addan, inda a halin yanzu sun rasa kusan fiye da kashi 80% cikin na taimakon da suke samu daga wadannan kasashe.