Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Ta'addanci A Arewacin Iraki
Wata Mota Shake da bama-bamai ta tarwatse a gabashin Takrit cibiyar jihar salahaddin dake arewacin kasar Iraki, lamarin da yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama.
Hukumar gidan telbijin da radio na kasar Iran ya habarta cewa a marecen jiya Talata ce motar da aka shaketa da bama-bamai ta tarwatse a cikin wata cibiyar tsaro ta kauyen Na'ima, lamarin da yayi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama.
A watan Maris na shekarar 2015 ne jami'ar tsaron kasar Iraki suka tsarkake kauyen Na'ima daga mamayar 'yan ta'addar kungiyar ISIS.
A cikin irin wannan yanayi, hare-hare gami da ta'addancin kungiyar IS ya rusa gine gine jihar Mausil, a halin da ake ciki gwamnatin kasar Iraki ta tura tawagwar jami'an tsaro na musaman domin warware bama-baman da kuma nakiyoyin da kungiyar IS suka dasa a yankin.