Yemen : Yara Miliyan 2 ke Fama Da Matsananciyar Tamowa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i22604-yemen_yara_miliyan_2_ke_fama_da_matsananciyar_tamowa
Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa yara kimanin miliyan biyu ne ke fama da matsananciyar tamowa a kasar Yemen.
(last modified 2018-08-22T11:30:27+00:00 )
Jul 26, 2017 14:23 UTC
  • Yemen : Yara Miliyan 2 ke Fama Da Matsananciyar Tamowa

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa yara kimanin miliyan biyu ne ke fama da matsananciyar tamowa a kasar Yemen.

Rahoton wanda na hadin gwiwa ne da hukumar lafiya ta Duniya WHO da asusun kula da yara kanana na Unicef da kuma hukumar kula da abinci ta duniya, bayan wani ran gadi na kwanaki uku da suka gudanar a wannan kasa ta Yemen.

Kimanin kashi 80% ne na yara ke bukatar agajin gaggawa wanda kusan miliyan biyu daga cikinsu ke fama da matsalar karamcin abunci.

Lamarin dai ya kara kamari ne a yayin da kasar ta Yemen ke fama da yaki da kuma cutar kwalera wacce ta yi sanadin mutuwar mutane 1.900 da kuma kusan mutane dubu dari hudu da suka kamu.

Kungiyoyin dai sun bukaci kasashen duniya dasu zage dantse domin taimakawa kasar ta Yemen.