An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Hizbullah Da 'Yan Ta'adda
(last modified Thu, 27 Jul 2017 12:17:40 GMT )
Jul 27, 2017 12:17 UTC
  • An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Hizbullah Da 'Yan Ta'adda

Rahotanni daga kasar Lebanon sun sheda cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin dakarun Hizbullah da kuma 'yan ta'addan takfiriyyah na Jabhat Nusra.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, 'yan ta'addan sun amince da dakatar da bude wuta da kuma neman a ba su damar ficewa daga yankin Jurud Arsal da ke gabashin Lebanon zuwa yankin Idlib na Syria.

Tun kafin wannan lokacin da Hizbullah ta ba su wa'adi na ficewa daga yankin, amma suka yi biris da hakan, lamarin da yasa Hizbullah ta dauki matakin yin amfani da karfi domin fatattakarsu tare da kwace kusan dukaknin yankunan da 'yan ta'addan suke iko da su a gabashin Lebanon a cikin kasa da mako guda, inda a halin yanzu mayakan Hizbullah suka killace su wuri guda, ta yadda ko dai su amince su mika kai ko kuma a halaka su, a kan haka ala tilas 'yan ta'addan suka amince da su ajiye makamnsu su fice daga yankin.

Rahoton na Almayadeen ya kara da cewa, a daren jiya dakarun Hizbullah sun gano wurin da jagoran 'yan ta'addan Abu Malik Altalli ya boye, kuma sun yi ruwan makaman roka  a wurin, wanda hakan na daga cikin dalilan da suka tilasta 'yan ta'adda mika wuya.

Dukkanin wuraren da dakarun Hizbullah suka tsarkake su daga 'yan ta'addan Takfiriyya, sukan mika iko da su ne ga rundunar sojin kasar Lebanon.