Sojojin Yemen Sun Mayar Da Martani A Kan Ta'addancin Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i22800-sojojin_yemen_sun_mayar_da_martani_a_kan_ta'addancin_saudiya
Sojoji da Dakarun sa kai na kungiyar Ansarullah na kasar yemen sun kai hari wuraren taruwar sojojin hayar saudiya a yankunan Asir, Jauf da Ta'az tare da hallaka da dama daga cikin su.
(last modified 2018-08-22T07:00:29+00:00 )
Aug 02, 2017 02:02 UTC
  • Sojojin Yemen Sun Mayar Da Martani A Kan Ta'addancin Saudiya

Sojoji da Dakarun sa kai na kungiyar Ansarullah na kasar yemen sun kai hari wuraren taruwar sojojin hayar saudiya a yankunan Asir, Jauf da Ta'az tare da hallaka da dama daga cikin su.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya habarta cewa dakarun tsaron kasar yemen sun halba makami mai lizzami mai lakabin Zilzal na biyu a wurin taruwar sojojin hayar saudiya a yankin Yakhtal na garin Almakha dake yankin Ta'az na kudancin kasar, lamarin da ya janyo hasara mai yawa ga makiya.

A wani harin bazata da Sojojin yemen din suka kaiwa Sojojin saudiya a yankin Asir dake kudancin saudiyar, sun hallaka da dama daga cikin su.

A bangare guda, jiragen yakin kawancen saudiya sun kai hari har so uku a yankin Alfar'i na garin Kataf dake jihar Sa'ada na arewacin yeman.

Tun a watan Maris na shekarar 2015 ne kasar Saudiya bisa goyon bayan kasar Amurka ta fara kai hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar kasar yemen tare da killace kasar ta sama, kasa da kuma ruwa, bisa da'awar medo da tsohon Shugaban da yayi murabus Abdu Rabahu Mansor Hadi, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar yamaniyawa sama da dubu 12 tare da jikkata wasu dubai na daban.