An Fara Musayen Fursunoni Tsakanin Hizbullah Da Jabhatun Nusra
Rahotanni daga kasar Labanon sun bayyana cewar an fara aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon din da kungiyar ta’addancin nan ta Jabhatun Nusrah, inda ‘yan ta’addan suka sako wasu dakarun kungiyar Hizbullah din su uku da suka kama a bangare guda kuma gwamnatin Labanon din ta sako ‘yan kungiyar su uku da take tsare da su.
Babban daraktan hukumar tsaron kasar Labanon din Birgediya Abbas Ibrahim ne ya sanar da hakan inda ya ce a nan gaba ma ‘yan ta’addan za su sako sauran dakarun kungiyar Hizbullah din su biyar da suke hannunsu bayan da motocin da take dauke da wasu dakarun ‘yan ta’addan da ake bude musu hanyar barin Labanon din sun isa kasar Siriya.
A kwanakin baya ne dai ‘yan ta’addan Jabhatun Nusra din suka bukaci da a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninsu da dakarun Hizbullah karkashin jagorancin Birgediyya Abbas Ibrahim din bayan shan kashin da suke ci gaba da fuskanta biyo bayan hare-haren da dakarun Hizbullah din suka kaddamar a kansu da nufin fatattakarsu daga yankin Arsal da suka mamaye shekaru 3 da suka gabata.
Yarjejeniyar dai ta kumshi cewa ‘yan ta’addan za su bar yankin zuwa lardin Idlib na kasar Siriya, su kuma a na su bangaren dakarun Hizbullah din za su dakatar da hare-haren da suke kai musu.