Wani Jami'in Tsaron HKI Ya Hallaka Sandiyar Hatsarin Jirgin Yakin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i22986-wani_jami'in_tsaron_hki_ya_hallaka_sandiyar_hatsarin_jirgin_yakin_kasar
Kafafen yada labaran Sahayuna sun sanar da faduwar jirgin yakin kasar a kudanacin yankunan mamaya na Palastinu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar matukin jirgin.
(last modified 2018-08-22T07:00:30+00:00 )
Aug 08, 2017 02:12 UTC
  • Wani Jami'in Tsaron HKI Ya Hallaka Sandiyar Hatsarin Jirgin Yakin Kasar

Kafafen yada labaran Sahayuna sun sanar da faduwar jirgin yakin kasar a kudanacin yankunan mamaya na Palastinu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar matukin jirgin.

Cibiyar sadarwar yankin Palatinu ta nakalto majiyar HKI na cewa a marecen jiya litinin wani jirgin yakin dakarun HKI mai saukar angulu samfarin Apache ya fadi a kusa da sansanin jiragen sama na Ramun dake kudancin yankin Palastinu da HKI ta mamaye, lamarin da ya yi sanadiyar hallakar matukin jirgin.

Kafin hakan dai, majiyoyin HKI sun sanar da mutuwa gami da jikkatar Sojojin su, sanadiyar hatsarin jirgin yakin kasar a kudancin yankunan mamaya.

Sansanin jiragen yakin HKI na Ramun na daga cikin mahiman sansanonin jiragen yakin HK a kudancin yankunan Palastinawa da HKI ta mamaye.