Rahoton MDD: Saudiyya Ce Ke Da Alhakin Kisan Yara A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i23316-rahoton_mdd_saudiyya_ce_ke_da_alhakin_kisan_yara_a_yemen
Majalisar dinkin duniya ta dora alhakin kisan daruruwan kananan yara a kasar Yemen a kan gwamnatin Saudiyya.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Aug 19, 2017 01:09 UTC
  • Rahoton MDD: Saudiyya Ce Ke Da Alhakin Kisan Yara A Yemen

Majalisar dinkin duniya ta dora alhakin kisan daruruwan kananan yara a kasar Yemen a kan gwamnatin Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, a cikin daftarin rahotonsa dangane da kisan fararen hula a kasar Yemen, ya bayyana cewa, Saudiyya ce ke da alhakin kisan mafi yawan kananan yara 1340 da suka mutu sakamakon rikicin Yemen.

Rahoton ya ce mafi yawan kananan yara da suka mutu sakamakon rikicin da ke faruwa a Yemen, sun mutu ne sakamakon hare-haren da jiragen yakin saudiyya suke kaddamarwa a gidajen jama’a, makarantu da kuma asibitoci gami da sauran wuraren hidimomin jama’a na yau da kulluma biranan kasar ta Yemen.

Daftarin rahoton na babban sakataren majalisar dinkin duniya yana kunshe da dalilai da dama da suke tabbatar da hakan, da suka hada da rahotannin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, da kuma kungiyoyin bayar da agaji masu zaman kansu, wadaanda komai yake faruwa a gaban idonsu.

An gabatar da wani rahoto wanda kungiyar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya tare da UNICEF suka hada kan kisan kananan yara a duniya, wanda suka bayyana cewa Saudiyya ta kashe kananan yara fiye da 600 a tsakanin 2015 da 2016 a Yemen, amma tsohon babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya cire sunan kasar ta saudiyya daga cikin rahoton, bisa abin da ya kira barazanar da ake yi ga rayuwarsa.