Basshar Asad: Mun Yi Galaba Akan Makarkashinyar Turai:
Shugaban kasar Syria wanda ya gabatar da jawabi a yau lahadi a birnin Damascuss ya ce; Tare da cewa Syria ta yi asara mai yawa, amma kuma ta murkushe makircin kasashen turai.
Basshar Asad ya kuma ce; Makiyan sun shelanta yaki ne akan Syria da zummar shimifda ikonsu akan yankin gabas ta tsakiya, sannan ya kara da cewa; Kwace iko da Syria, yana nufin shimfida iko akan gabas ta tsakiya, kuma duk wanda yake ido da gabas ta tsakiya zai yi tasiri a siyasar duniya.
Shugaba Basshar Asad ya kuma jinjinawa jamhuriyar musulunci ta Iran akan taimakawa kasarsa a fada da ta'addanci, haka nan kuma kungiyar Hisbullah ta lebanon.
Basshar Asad ya ce; yin gwagwarmaya duk da wahalhalun da suke tattare da shi, ya fi sauki akan mika kai ga makiya.