Jiragen Saman Masarautar Saudiyya Sun Kashe Mutane 35 A Kasar Yamen
Jiragen saman yakin Masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan wani sansanin 'yan gudun hijira a shiyar arewacin birnin Sana'a fadar mulkin kasar Yamen, inda suka kashe mutane akalla 35 tare da jikkata wasu na daban.
Gidan talabijin na Al-Masirah na kasar Yamen ya watsa rahoton cewa: Da jijjifin safiyar yau Laraba jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta a yankin Baitul-Aza da ke garin Arhab a shiyar arewacin birnin Sana'a fadar mulkin kasar Yamen, inda suka mutane akalla 35 tare da jikkata wasu 15 na daban.
Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun maida martani ta hanyar harba makamai masu linzami kan matattaran sojojin hayar masarautar Saudiyya da ke shiyar arewa maso gabashin yankin Kahbub a lardin Lahaj a kudancin kasar ta Yamen, inda suka kashe tare da jikkata sojojin hayar masu yawa. Kamar yadda sojojin na Yamen suka tarwatsa motar yakin Saudiyya mai sulke a yankin Al-Hayajah da lardin Al-Juf a shiyar arewacin kasar ta Yamen.