Aug 23, 2017 18:59 UTC
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Suka Kan Sabon Matsayin Kasar Sudan Dangane Da Palasdinawa

Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ya yi Allah wadai da furucin ministan harkokin sayan hannun jari na kasar Sudan kan al'ummar Palasdinu.

A bayanin da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta fitar a yau Laraba yana dauke da Allah wadai kan furucin Mubarak Fadhil ministan harkokin sanya hannun jari na kasar Sudan kan al'ummar Palasdinu musamman kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa tare da bayyana furucin a matsayin wofantar da kimar al'ummar Sudan da ma al'ummar musulmi da na Larabawa baki daya.

A jiya Talata ce jaridar Yahudawan Sahayoniyya ta Ha'aresz ta buga furucin Mubakar Fadhil ministan harkokin sanya hannun jari na kasar Sudan na goyon bayan gwamnatin Sudan kan kulla alaka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da yin da'awar cewa: Matsalar Palasdinawa ta janyo koma baya a harkokin ci gaban kasashen Larabawa.

Tags