Bukatar Fira Ministan Hukumar Palasdinawa Ga Majalisar Dinkin Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i23658-bukatar_fira_ministan_hukumar_palasdinawa_ga_majalisar_dinkin_duniya
Fira ministan hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarta wajen kawo karshen bakar siyasar zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu.
(last modified 2018-08-22T11:30:37+00:00 )
Aug 29, 2017 18:57 UTC
  • Bukatar Fira Ministan Hukumar Palasdinawa Ga Majalisar Dinkin Duniya

Fira ministan hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarta wajen kawo karshen bakar siyasar zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu.

A taron manema labarai da ya gudanar da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a garin Ramallah na Palasdinu a yau Talata: Fira ministan hukumar cin kwarya-kwaryar Palasdinawa Rami Hamdallah ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana ci gaba da mamaye yankunan Palasdinawa a birnin Qudus da gabar yammacin kogin Jordan ta hanyar gudanar da gine-ginen matsugunan Yahudawan Sahayoniyya 'yan kaka gida tare da ingiza tsagerun Yahudawan Sahayoniyya kan mamaye Masallacin Qudus mai alfarma.

Rami Hamdallah ya kara da cewa: Dole ne a kan Majalisar Dinkin Duniya ta yi iyaka kokarinta domin ganin an samar da yantacciyar kasar Palasdinu da zata rayu kafada da kafada da haramtcciyar kasar Isra'ila.

A nashi bangaren babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi furuci da cewa: Gine-ginen matsugunan Yahudawan Sahayoniyya 'yan kaka gida a yankunan Palasdinawa, kokari ne na neman yin kafar ungulu ga shirin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Palasdinu.