Dakarun Tsaron Yemen Sun Kai Harin Rokoki A Kan Sojojin Saudiya
Sojoji da dakarun sa kai na kasar yemen sun kai harin rokoki a kan wuraren taruwar sojojin saudiya a najran dake kudancin saudiya a daren jiya laraba.
Tashar telbijin din Al-alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin tehran ta nakalto wata majiyar tsaron yemen na cewa Dakarun tsaron kasar sun harba wasu rokoki kirar Katyusha a wuraren taruwar dakarun tsaron saudiya a sansanin Akifa dake kudancin Saudiya.
Har ila yau Dakarun tsaron yemen din sun yi taho mu gama tare da sojojin hayar saudiya a jihar Ma'arib dake tsakiyar kasar, a yayin taho mu gamar dakarun kasar ta yemen sun samu nasarar hallaka Sojojin hayar saudiya guda 10.
A jiya Laraba ma, harin kwantan bauna da dakarun tsaron kasar yemen din suka kaiwa sojojin hayar saudiya a garin Tibet al-Matar dake jihar Ma'arib ya janyo hasara mai yawa ga sojojin hayar saudiyan.
A bangare guda, jiragen yakin kawancen saudiyar sun ruwan bama-bamai a yanki na tara dake birnin sana'a fadar mikin kasar.
Yaki wuce gona da iri na kasar Yemen ya fara ne tun daga watan Maris din 2015, kuma ya zuwa yanzu yayin sanadiyar mutuwar yamaniwa dubu 12.