Ganawar Ministan Tsaron Rasha Da Shugaba Asad Na Siriya
(last modified Wed, 13 Sep 2017 05:51:31 GMT )
Sep 13, 2017 05:51 UTC
  • Ganawar Ministan Tsaron Rasha Da Shugaba Asad Na Siriya

Ministan harakokin tsaron Rasha ya gana da Shugaba Bashar Al-asad na Siriya a birnin Damascus.

A jiya Talata, Ministan tsaron kasar Rasha Sergey Shoigu ya kai ziyara kasar Siriya inda ya gana da Shugaba Bashar Al-asad, inda suka tattauna34 kan mahiman batutuwan da suka shafi tsaro da kuma kara bunkasa alakar tsaro dake tsakanin kasashen biyu.

Rahoton ya ce bangarorin biyu sun tattauna a kan irin nasarorin baya-bayan nan da dakarun kasashen biyu suka samu a yaki da 'yan ta'addar ISIS a Siriya da kuma yadda za a shigar da kayan agaji a yankunan da aka tsarkake a kasar ta Siriya.

A karshen watan Satumba ne kasashen Siriya da Rasha suka amince a kan yin aiki tare wajen yakar 'yan ta'adda a kasar ta Siriya, inda kasar ta Rasha ta tura dakarun tsaron sama da na ruwa domin taimakawa dakarun tsaron siriya wajen yakar 'yan ta'adda a kasar.

Tun a shekarar 2011 ne kasar ta Siriya ta fada cikin rikici, inda kungiyar 'yan ta'adda daga kasashe daban daban na Duniya suka shiga kasar bisa goyon bayan saudiya da Amurka tare da kawayenta, inda suka mamaye garuruwa da dama na kasar, to sai dai bayan shigar mayakan Hizbullah na Labnon, Sojojin na Siriya sun samu nasara kwato sama da kashin 85% na yankunan da kungiyoyin 'yan suka mamaye.